ss TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION WANDA AKA SAKE GYARA A SHEKAERA TA 2020 1. GABATARWA Mun yarda mu gabatar da wannan tsarin dokoki da ka’idoji domin kebe sharuddan bangaskiya, domin tafiyadda ayyukan wannan association bisa ka’idar Nigerian convention, da kebe yancin kowace ikilisiyya dake member, da ‘yancin association domin tafiyadda dangantaka da sauran association. 2. SUNA Wannan association za’a cigaba da kiran sa da suna Malumfashi Baptist Association. 3. TAKE Maganan Allah karfi ce agaremu (I korintiyawa 1:18) the word of God is power on to us I corint. 1:18 4. MEMBOBI DA YANKI Wannan association ya kunshi ikklisiyoyi da Unguwannin wa’azi kafaffun ikklisyoyi guda 6, da unguwanin wa’azi guda 11 dake a kananan hukumomi guda (3) wadanda suka hada da Malumfashi, Kafur Da Musawa. 5. DALILAI DA MUNUFOFI a. Domin yin sujada da zuminci ta wurin bishewar ruhu maitsarki. b. Domin jaddada bishara gida da waje 1|Page TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION c. Domin mu sadaukarda jikimu da mallakarmu don cigaban association. d. Domin magance matsaloli dake iya faruwa acikin ikklisiyoyi. e. Domin taimakawa ayi girma cikin ruhaniya tawajen bita da koyaswa. f. Domin hada hannu da conference da convention don su cimma manufofinsu. 6. FURCI BANGASKIYA a. Mun bada gaskiya littafi mai tsarki shine tushe iko cikin daukan abu b. Mun bada gaskiya cewa Allah ne mahliccin sama da kasa, mun yarda da uku cikin daya (Trinity) Alllah Uba Allah Da Allah Ruhu Mai Tsarki. c. Mun yarda Yesu Kristi dan Allah ne maiceton mu shine shugaban mai shara’a a rana ta kaeshe. d. Mun amince ruhu mai tsarki shine maitaimakonmu. Mai bishemu. e. Mun yarda da Baptisma ta nutsarwa a cikin ruwa da sunan Uba dana Da dana Ruhu maitsarki f. Mun yarda da memba mai Baptisma ya karbi jibin Ubangiji. 2|Page TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION g. Wannan association bata yarda da membobi su shagiyaba da sayarwa, bata yarda aba membobi susha taba ba don laifine doka zata hau wanda yayi hakan. h. Wannan association bata yarda aba wani wanda yake cikin kungiyar matsafa, ko asiri ko mai mata biyu ko mai dodo da sauran kungiyoyi shaidan wani matsayiba a iklisiya ko association, idan an san haka kada a yarda yarike wani shugabanci a ikklisiya. 7. GUDANARWA a. Wannan association ta amince da taro sau hudu a shekara za’a rinka zagayawa ikklisyoyi dabam-dabam a cikin wannan association. b. Ikklisiyoyi, kungiyoyi da kwamitoci zasu rika bada rahontanninsu a lokacin taron association. c. A taron association za’a rinka yin wa’azi da baiko da koyaswa. 8. MA’AIKATA:- ma’aikatan wannan association sune: I. Maikujear (moderator) II. Mataimakin maikujera (Ass. moderator) III. Marubuci (Secretary) IV. Mataimakin marubuci (Ass. Secretary) V. Ma’aji (Teasurer) VI. Marubucin kudi (Fin Secretary) VII. Mai duba ajiya (Aiditor) 3|Page TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION VIII. Shugaban ilimin nmanya (literacy class) IX. Shugaban bishara X. Shugaban zumuntar maza (M.M.U) XI. Shugaban zumuntar mata (W.M.U) XII. Shugaban matasa (youth leader) XIII. Maibada shawara (advisor) AIKIN MA’AIKATA NA ASSOCIATION 1. MAIKUJERA (MODERATOR) ya zama reverend ne shi. a. Zai shugabanci tarukan association. b. Shine mai bada umurnin kiran taron kwamintin zartaswa. c. Shine mai wakiltar association a taron kwamitin zartaswa na conference. d. Zai zama mashawarci ga dukan kungijyoyi na association ya kuma zama mai kai ziyara ga kowace kungiya. e. Zaiyi shekara (3) a association kafin a zabeshi ya zama moderator f. Hakkinsane ya rika ziyara ga ikklisiyoyi na association. g. Zai zama daya daya daga cikin masu sa hannu a takardar banki h. Zai iya sa wani ya wakilceshi a wasu tarurruka ko kuma ya wakilta membobinsa a wasu tarurruka. 4|Page TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION i. Aikin sane ya wayarwa ikklisiya kai game da matakan da suka dace subi kamar kiran Pastor, sujadar karba, sujadar bankwana, sujadar kebewa ta Pastor zuwa Reverend. 2. MATAIMAKIN MAI KUJERA (shima yazama Pastor ne) a. Zai dauki matsayin shugaba idan bayanan. b. Zai taimakawa shugaba a cikin aikinsa. c. Shine makujeara na kwamitin zaben ma’aikata na Association da sauran kwamitoci da ka iya tasowa. 3. MARUBUCI (SECRETARY) zai iya zama Pastor ko memba. a. Shine mai daukar rahoton association dan kwamitin zartaswa na association. b. Shine mai ajiye dukkan rahotonin na tarukan association. c. Zai zama maibada rahoto a dukkan taron association, na zartaswa ko na jama’a baki daya. d. Shine mai aikawa wasikun taro na association. 4. MATAIMAKIN MARUBUCI (ASST. SECTRETARY) zai iya zama Pastor ko memba. a. Zai dauki matsayin marubuci idan bayanan. b. Ya iya wakiltar marubuci a wasu tarurruka c. Shi membane na kwamitin zaben ma’aikata na association d. Shi membane na kwamitin zartaswa na association 5|Page TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION 5. MA’AJI (TREASURER) Ya kasance memba mai cikakkiyar shaida ta ruhaniya. a. Zai karbi kudi ya adana, ya kuma biya dukan kudaden da association ta amince dasu a biya. b. Zai ajiye amintaccen rohoton kudi na association tare da shiga da fitarsu. c. Zai bada rahoton kudi a lokutan taron association. d. Zai kasance daya daga cikin yan kwamiti na association. e. Shi memba ne a kwamitin kasafin kudi. f. Zai zama mai bada shawara akan yadda za’a kasha kudin association g. Yana daya daga cikin masu sa hannu a takardun banki. 6. MARUBUCIN KUDI (FINANCIAL SECRETARY) ya zama wanda ya iya karatu da rubutu mai shaida ta ruhamaniya a. Shine mai karbar kudaden a taron association yaba ma’aji b. Shine mai ba kowace iklisiya rasidi (receipt) c. Aikinsane yaba ma’aji rasidin (receipt) fitarda kudi d. Shima yana cikin membobin kwamiti na association 7. MAIDUBA AJIYA (AUDITOR) a. Zai zama mai kula da ydda ake kasha kudi na association 6|Page TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION b. Aikinsane ya bada shawara na harkokin kudin association. c. Zai iya yarda ko yaki yarda da rahoton kudi a lokacin taron association d. Memebane shi a kwamitin zartaswa 8. SHUGABAN ILIMIN KRISTA (LITERACY CLASS) Wannan sashi ya kunshi Sunday school, CTP da kuma yaki da jahilci a. Aikin shine ya ziyarci ikklisiyoyi na association domin yaga cigaban Sunday school da CTP b. Aikin sane ya bada rahoto a taron association c. Aikin sane yabada shawarwari a cikin iklisiyoyi daya ziyarta da kuma a taron association d. Zai shirya bita domin shugabannin CTP da Sunday school na iklisiyoyi e. Zai wakilci association a taron CTP da Sunday school na conference dana convention (NBC). f. Aikin shine ya kafa ya kuma karfafa yadda za’a kafa azuzuwan yaki da jahilci a ikklisiyoyi domin koyarda karatu da rubutu ga manya g. Aikin sane ya bude ajujuwa tare da malamai h. Zai ziyarci ajujuwa da ya kafa domin yaga ci gabansu 9. SHUGABAN GIRMAN IKLISIYA (CHURCH GRIWTH) ya zama shi Pastor ne 7|Page TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION a. Aikin shine yaga an kafa kungiyar shelar bishara a kowace iklisiya b. Aikin shine ya hada hannu da kungiyoyin shelar bishara na iklisiyoyi domin su cima burinsu na kafa sababbin iklisiyoyi c. Aikin shine ya rika ziyartar iklisiyoyi da aka bude. d. Zai bada rahoto a taron association kowace kwata 10. SHUGABAN ZUMUNTAR MAZA (MEN’S MISSIONARY UNION) a. Ya zama membane na M.M.U a ikklisiyarsa ya kuma zama wanda an maya haihuwarsa ta ruhaniya. b. Zai zama mai karfafa kungiyoyi na zumutar maza da R.A a iklisiyoyi da association c. Zai shirya bita in akwai bukata domin kungiyoyin zumuntar maza dake cikin iklisiyoyi na association d. Zai bada rahotun aikinsa a taron association 11. SHUGABAR ZUMUNTAR MATA (WOMEN MISSIONARY UNION) ta kasance matar Pastor wadda ta sami horaswa a makarantar Pastor a. Aikinta ne ta tabbatar cewa kowacce ikliasiya akwai jam’iyar mata masu shelar bishara b. Aikinta ne ta tabbatar cewa mai ziyara ta association tana aikinta 8|Page TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION c. Zata wakilci association a taron conference da convention. d. Itace mai kiran taron association na mata e. Zata tabbata iklisiyoyi suna hidima ga kowa tareda aika rahoton hidimarsu. 12. SUHUGABAN MATASA (YOUTH LEADER) ya zama mutum mai ruhaniya. a. Ya zama memba na matasa a iklisiyarsa b. Zai rinka ziyartar iklisiyoyi domin ya karfafa kugiyar matasa ko kafawa. c. Ya tabbatar ya shirya daren matasa a lokacin taron association d. Ya tabbatar ya bada rahoto a taron association e. Zai tabbatar da kowace iklisiya ta gabatar da makon matasa na kowane shekara 13. MAI BADA SHAWARA KO MASHAWARCI ASSOCIATION a. Ya zama Pastor wanda ya sami dandanawar aiki b. Zai kasance memba a kwamitin association MEMBOBIN KWAMITIN NA ASSOCIATION 1. Maikujera (Moderator) 2. Mataimaki mai kujera (Ass. moderator) 3. Marubuci (secretary) 4. Mataimakin marubuci (Asst. secretary) 9|Page NA TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION 5. Ma’aji (treasurer) 6. Marubucin kudi (financial secretary) 7. Maiduban ajiya (auditor) 8. Shugaban ilimi krista (literacy class) 9. Shugaban girman iklisiya (church growth) 10. Shugaban zumuntar maza (MMU) 11. Shugaban zumuntar mata (WMU) 12. Shugaban zumuncin pastoci 13. Dukan pastocin association da suka sami horaswa a makarantun tauhidi na Baptist 14. Shugaban matasa (youth leader) 15. Mai bada shawara. 14. TSAWON LOKACIN MA’AIKATA a. Dukan ma’aikatan association zasu yi shekaru uku (3) gaba dayansu, amma akwai yiwuwan mutum ya sake komawa karo na biyu. b. Wanda yayi rashin aminci a aikinsa za’a shawarceshi, in yaki ji to za’a chanzashi. c. Mutum daya bazai rike aiki / mukami biyu iri daya lokaci guda a matakin association da conference ba. d. Duk wanda za’a zaba a matakin association dole ya zama yana bada gudummuwarsa a iklisiyuarsa ta gida. 10 | P a g e TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION 15. HIDIMAR PASTOR A CIKIN ASSOCIATION a. Sabon Pastor daga makarantar tauhidi ta Baptist, ba za,a zabeshi wani aiki ko yayi wata hidima ba, associoation sai sai yayi shekara biyu (2) b. Sabon Pastor daga wata iklisiya, ba za’a zabeshi ko yayi wata hidima ba a association sai yayi shekara daya 1 c. Moderator (mai kujera) wanda za’a zaba a matsayin moderator dole ya kasance a association na tsawon shekaru uku 3 d. Duk Pastorn da ba’a karbe shi ba, ba zai yi aiki a association ba. 16. CIKE GURBIN MA’AIKATA Idan daya daga cikin ma’aikata na association ya sami canjin wurin aiki ko ya rasu ko yayi rashin aminci, kwamitin zartarwa (EC) zasu iya kawowa gida. Gida zasu kafa kwamitin zaben cike gurbin da wani. 17. MIKA KAYAN AIKI a. Wajibine, tsohon ma’aikaci ya bada rahoto tare da mika kayan aiki ga sabon ma’aikaci b. Sabon ma’aikaci za’a bashi kayan aiki a taro na hudu na shekara, wato kwata ta hudu 4 11 | P a g e TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION 18. KIRAN PASTOR DA WASU SUJADAI i. KIRAN PASTOR: dukan iklisiyar data shekara uku da budewa ya kamata ta kira makiyayi. a. Iklisiyar da paston ta ya tashi kada ta wuce wata 6 bata kira wani ba don aiki ya cigaba. b. Zasu iya kira daga makarantar masu wa’azi ko wasu association, conference. c. Idan Pastor ya amsa kiran iklisiya sai ta sanarwa association, conference, convention, idan kuma kiran daga makarantane iklisiyar zata sanarwa da makaranta ii. SUJADAR KARBA: kada Pastor ya wuce wata shida6 ba’a karbe shi ba, domin ya sami damar tafiyar da aikin da aka bashi. Ikilisiyar da take shirin kiran Pastor, in har ya amince zaizo to iklisiya zata shirya karbar shi a lokacin zuwansa wato dayazo a karbeshi. iii. SUJUDAR SALLAMA: ya kamata kowace iklisiya ta shirya sujudar bankwana ga pastonta idan zai barta. iv. SUJUDAR KEBEWA: iklisiyar da taga pastonta ya cancanci kebewa bari ta nemi shawarar yin haka. v. SUJUDAR NUNA GODIYA: bisa ga tsarin conference bari kowace iklisiya ta shirya sujadar nuna godiya kowace shekara. 12 | P a g e TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION a. Bisa ga tsarin Nigerian Baptist convention bari kowace iklisiya ta shirya kasaitacciyar sujadar nuna godiya ga pastonta bayan shekara biyar 5 inda zata gayyaci mutane daga waje. 19. KWAMITOCI Association na da ikon kafa kwamiti idan bukatar hakan ta taso. 20. HANYOYIN MAGANCE MATSALOLI A IKLISIYA Idan wata matsala ta taso a cikin ikilisiya bari a sasanta a cikin iklisiya, idan kuma tafi ko ta gagara sai a kaita ga association, idan nan ma ya gagra sai a kaita conference, idan nan ma ta gagara sai akaita ga convention. 21. HORO a. Horo zai kasance an sami wani ko wata da irin wadanna halaye: sata, fasikanci, zina, shiga kungiyar asiri da sauransu. Iklisiya tanan iya bashi horo. Iklisiya zata iya tada horo bisa ga irin laifin da mutum yayi idan yana da matsayi a cikin iklisiya za’a cireshi, bayan kuma yagama horo za’a koma dashi, amma ba akan aikinsa ba ko matsayin sa a iklisiya ba. – idan memban iklisiya yayi laifi ya kuma gane laifinsa ya tuba, a yafe mashi/mata. b. Idan Pastor yayi laifi, iklisiya zata iya zama da yan kwamiti su tattauna don su magance matsalar da 13 | P a g e TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION sauri. Tare da bin matakan Nigerian Baptist Convention. KA’IDOJIN NA ASSOCIATION a. Wajibine iklisiya ta yiwa wadanda suka tuba baptima don su zama membobi cikakku. b. Wajibine iklisiya taci jibin Ubangiji akalla sau hudu a shekara. c. Ya kamata wadanda zasu yi aure suje asibiti a gwada su don aga lafiyarsu kafin a daura masu Aure. d. Wajibine budurwa da saurayi ayi masu Baptisma kafin a daura masu aure e. Iklisiya ba zata shiga hidimar wanda ya saki matarsa ba idan zai sake aure f. Kungiyar mawakan sabon rai bata. Bisa ga tsarin Nigerian Baptist Convention sai dai Kungiyar girman iklisiya aka sani. g. Bisa ga tsarin Nigerian Baptist Convention ba kungiyar yammatan jiya sai dai kungiyar jam’iyar mata masu shelar bishara h. Wajibine ga ma’aurata wajen sa ranar bukinsu ya kasance kwana biyar kafin ranar Christmas da kuma kwana biyar bayan Christmas 14 | P a g e TSARIN DOKOKIN MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION i. Duk wanda za’a zaba a wata kujera/mukami a association sai iklisiyarsa ta amince dashi. j. Duk wanda zai yi Magana ko ya bada shawara a lokutan taron association dole sai wanda yayi regista. k. Dokace ga Association ta rinka ba moderator alawus. 22. GYARE-GYARE a. Idan akwai bukatar gyara za’a mikashi a rubuce zuwa ga kwamitin zartarawa na association. b. Gyaran da za’a yi, kwamitin zartarwa zai mika bukatar ga jama’a a taron association domin tattaunawa. c. Gyaran kaidodi zai rinka zuwa a duk bayan shekara uku 3 (constitutional review) LOKACIN FARA AIKIN DOKOKIN DA KA’IDODI Wannan tsarin dokaki zai fara aiki bayan da jama’a sun karba a taron association. GA SUNAYEN WADANDA SUKA SAKE GYARAN WADANNAN DOKOKI NA MALUMFASHI BAPTIST ASSOCIATION 1. Rev. Sama’ila Bido Kwasau - Chairman 2. Rev. Matthew P. Biwet - Member 3. Rev. Yohanna Haruna Mwolchuk - Member 4. Rev. Jonathan Haruna - Member 5. Dcn. Yunana Yusuf - Member 6. Lami Kabir - Member 7. Ibrahim Luka - Secretary 15 | P a g e